Sunday, October 14, 2018

Pfizer Trovan Victims Forum and Pfizer laxities

RA’AYIN #RARIYA: Pfizer: Da Sauran Rina A Kaba

Har yanzu tana kasa tana dabo a jihar Kano sakamakon gwajin maganin nan (TROVAN) da babban kamfanin nan mai yin magunguna na kasar Amurka mai suna PFIZER ya gudanar ba akan doka ba. Shugaban kungiyar wadanda abin ya shafa, Malam Mustapha Maisikile ya ce za su koma kotu domin neman hakk-insu akan kamfanin da ya yi gwaji akan ’ya’yansu. A ta bakin Maisikeli ya ce ainihin wanda abin ya shafa ba a ba su diyyar ’ya’yansu da suka rasa rayukansu ba a sakamakon wannan gwaji da kamfanin Pfizer ta gudanar ba, wasu ne can suka yi dumu-dumu akan wannan kudi da kamfanin Pfizer ta bayar bayan kotu ta sulhunta.

A takaice ga abin da ya faru akan wannan gwaji :

1. A shekarar 1996 ne aka sami annobar cutar sankarau a Kano sai shahararren kamfanin nan na Amurka mai yin magunguna mai suna PFIZER ya yi amfani da wannan damar ya yi gwajin sabon maganinsa mai suna TROVAFLOXACIN, wanda aka fi sani da TROVAN. Wanda yayi sanadiyyar mutuwar yara kusan dari (100). Yayin da wasu da yawa kuma suka sami nakasa wanda ya hada da rashin ji, da rasa wasu gabobi wanda suka hada da hannu da kafa da tabin kwakwalwa.

2. A mayun shekara ta 2006 ne kwararrun likitoci suka gudanar da bincike a game da gwajin maganin nan TROVAN wanda kamfanin ya gudanar a kan yara 100 da jarirai na kamfanin PFIZER. Binciken na su ya gano kamfanin ya gudanar da binciken na sa ba a kan ka’ida ba, kuma maganin ba a yi masa rijista ba, wanda hakan ya saba wa dokar Nijeriya da dokar kasashen waje musamman dokar HELSINKI wadda take tattatare da yadda likitoci za su gudanar da bincikensu. Rahotan binciken ya nuna gwamnatin Nijeriya ba ta ba da damar a gudanar da wannan binciken ba. Domin takardun da wanda yake shugabantar binciken wani dan Nijeriya ya gabatar a lokacin , sai daga baya aka gano na bogi ne.

3. A watan Janairun sheka¬ra ta 2009 ne kotun daukaka kara ta kasar Amurka ta yarda da ’yan’uwan wadanda aka yi wa gwajin maganin TROVAN na kamfanin PFIZER da su shigar da kara a kasar Amurka bayan kokarin da suka ringa yi tun farko bayan faruwar abin.

4. Gwamnatin jihar Kano tare da gwamnatin tarayya sun shigar da kara suna mai neman kamfanin PFIZER ya biya diyyar dala bili-yan biyu da dala bilyan shida ga wanda abin ya shafa.

5. Daga karshe kamfanin PFIZER ya yarda a sasanta bayan wasu manyan masu fada-a-ji a Nijeriya sun shigo maganar, irinsu tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon. Kamfanin na PFIZER ya yarda ya biya diyyar dala milyan saba’in da biyar (75). Wanda daga cikin kudin dala milyan talatin da biyar(35) za a raba tsakanin wadanda abin ya shafa. Inda kowane yaro da a ka yi gwajin akan sa zai sami dala dubu dari da sabainda biyar (175). Yayin da dala miliyan talatin (30) za ta tafi ga gwamnatin jihar Kano domin gina asibiti.

Wasa farin girki kenan ga wad-anda wannan kaddara ta afka wa, tunda har yanzu tsuguno bai kare masu ba. Tun da a yanzu suna kokarin komawa kotu domin ta bi masu hakk-insu da aka danne masu. Me ya sa har yanzu ba a biya su diyya ba? Kamar yadda aka yi yarjejeniya tsakanin wanda abin ya shafa, gwamnatin Jihar Kano da kamfanin PFIZER. Ana wata sai ga wata kuma, kamfanin PFIZER ya ce sai an gudanar da gwajin kwayoyin halatta ga yara dari da casa inda biyu (192) da aka yi gwajin maganin akan su. Amma su wadanda abin ya shafa suna ganin kamar wasa da hankali kamfanin zai masu domin ka da ya biya su diyya , wanda hakan ya saba wa yarjeninyar da suka yi tun farko. Kuma suna ganin anya kamfanin zai yi gwajin gaskiya da ainihin kwayoyin halittar da aka dauka na wadanda abin ya shafa?

Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwuiwar kamfanin PFIZER sun bude asusun taimakawa masu fama da ciwon sankarau wanda tsohon mai sharia Bashir Wali ke shugabanta. Rahotanni daga majiya mara tushe sun nuna cewar shugabannin da suka kafa wannan asusu su bakwai suna karbar naira dubu dari hudu a kowanne zama da suke yi, amma wadanda abin ya shafa ba a biya su diyya ba. Haka kuma an yi zargin shugabannin da suke wakiltar yaran da aka yi wa gwajin maganin TROVAN an ba su cin hanci a yayin da suka yi wani zaman sasantawa a birini Landan. Dalilin ba da cin hancin kuwa ba zai rasa nasaba da dakile diyyar da za a bayar ba.

Rariya tana ganin babban kamfani kamar PFIZER ace ya hada baki da wasu ’yan Nijeriya an yi gwajin magani wanda ba a yarda da shi ba kuma akan yara kanana a garin Kano wanda ba su da hakkin kowa a kansu, ba su ji ba, ba su gani ba, bai kamata ba. Sakamakon wannan gwaji ne yara da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka sami nakasa da har abada babu warkewa ko kuma magani. A sakamakon son zuciya, rashin kula da kabilanci na kamfanin PFIZER. Iyaye sun rasa ’ya’yansu har abada, wadAnda suka nakasta kuwa an tauye masu rayuwa.

Abin bakin ciki wannan sai ya zama kamar wata dama ce da wasu ’yan Nijeriya da shugabanni suka samu domin kara wa kan su kudi, kudin ma haramtacce, don ganin an danne wa wadanda aka zalunta hakkinsu. Wannan rashin adalci da rashin imani da me ya yi kama? A sakamakon haka ne kungiyar da abin ya shafa suke ganin kamfanin ya kamata ya amsa masu wasu tambayoyi, misali, me ya sa aka kirkiro wata hukuma aka damka mata amanar kudin mutane ba tare da yardarsu ba?

Wani kamfani mai zaman kansa da kamfanin PFIZER ta ba wa kwangilar gwajin kwayoyin halittar da wadanda abin ya shafa mai suna BODE TECHNOLO¬GIES an zargi kamfanin PFIZER da hada baki da wannan kamfani da ka da ya bada sakamakon dai-dai da zai tabbatar da cewa wad-anda abin ya shafa su din ne dari bisa dari. Ta yadda kad-an daga cikin wadanda abin ya shafa za a ce sun tsallake gwajin. Kuma wannan kamfani na BODE TECHNOLOGIES ya san cewa wannan ya saba ka’idar gwajin da ake amfani da shi a kasashen waje. Wannan ya tabbatar da zar¬gin wadanda abin ya shafa cewa kamfanin PFIZER ba zai yi masu adalci ba idan aka yi wannan gwaji na kwayoyin halitta. Wanda hakan kuma ya saba wa doka, ya kuma nuna kamfanin PFIZER ita ce alkalin kanta.

Sunan Nijeriya dai ya sake baci a idon duniya. Hakkin al ’ummarta da kula da lafiyarasu da yake rataye a wuyanta ta kasa tabuka komai wajen hanawa a yi wannan gwajin a kan ’yan kasarta, ko kuma yanzu da abin ya faru ta kasa yin komai don ganin ta kwatar wa wadanda abin ya shafa hakkinsu, sai ma zargin yin dumudumu da babakere da handama da wasu suka yi a kan kudin. Hhmn! Abin ma rainin wayo ne kamfanin PFIZER ya isa ya je kasashen Turai irinsu Ingila da Amirka ya yi wannan gwajin? Ina! Ya san a can sai ya biya makudan bilyoyi masu ciwo ba kamar a nan ba da zai biya ’yar dala milyan saba’in da biyar shikenan zance ya mutu. Ko kun san ma maganin TROVAN na kamfanin PFIZER an hana amfani da shi a kasashen Turawa da Amurka? Sai daga baya hukumar kula da abinci da magani (FDA) ta yarda a ringa amfani da shi ga manya amma ban da yara ’yan kasar Amurka a shekarar 1997. Ko yanzu lokaci bai kure wa shugabanninmu ba. Wannan rashin adalci da aka yi wa wadanda abin ya shafa, kuma abin kunya ne a idon duniya a ce da sanin wasu manya aka hada baki aka yi wannan gwaji kuma dan kudin diyyar da bai taka kara ya karya ba shi ma ana so a lamushe. Saboda haka hakkin gwammnati ne ta fara sabon bincike akan wannan maganar da bin diddigin yadda abin ya faru tun farko har kawo izuwa maganar bin diyya da yadda aka raba kudin. Kusan shekara goma sha bakwai ana abu daya, wanda aka cuta an dai cuta kawai, wata shari’ar sai a lahira.

No comments:

Post a Comment