Friday, February 22, 2019

Makafi akan tsaunin tsayau, kilimanjaron Africa ga girma ga tsawa ga nisa

BBC News Hausa menu Makafin da ke hawa Tsaunin Kilimanjaro 21 Fabrairu 2019 Aika wannan shafi Email Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Whatsapp Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS A ranar 20 ga watan Fabrairu, makafi bakwai da 'yan jagoransu hudu suka karasa tattakin da suka yi mai nisan mita 5,750 zuwa tsaunin Kilimanjaro a kasar Tanzania. Masu tattakin sun shafe sa'o'i tara kafin hawa kololuwar tsaunin inda suka shafe mita 914. A lokacin hawan nasu, sun ta fama da iska, da matsanancin sanyi, suna gab da isa ne suka hango wani jirgin sama yana wasa da fuffukensa inda yake sara masu a kan namijin kokarin da suka yi. Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS An kirkiro wannan tattakin ne domin nunawa duniya cewa makafi da ke Afirka ba wai sun gaza ba ne, ''idan aka horar da su suna da juriya da kwarin gwiwar gudanar da abubuwan birgewa.'' Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS Mutum takwas ne suka fara wannan tattakin amma a daren 19 ga watan Fabrairu bayan sun sha wa wahalar hawa duwarwatsu sai suka yada zango a wani kogo, daga nan ne daya daga cikinsu ya fita daga cikin masu tattakin. Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS Geoffrey Salisbury na kungiyar makafi ta kasashen rainon Burtaniya ya ce ''a wannan ranar, mun sha fama da ciwon kafa kuma mutum biyu sun yi fama da rashin lafiya sakamakon jiri da suka sha bayan hawa wuri mai tsayi.'' ''A karon farko mun tarar da ruwan kankara. Na hau saman kankarar, na fasa tsinin kankarar na kawowa John Opio mai fama da ciwon kai.'' ''Tsananin sanyin kankarar ya tsoratar da shi har ya sa ya manta cewa ba shi da lafiya.'' ''Ya hau da karfinsa amma daga baya ya sare sakamakon rashin cikakkiyar lafiyar ci gaba.'' Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS An zabi wadanda suka yi tattakin ne daga daruruwan 'yan sa kai a Kenya da Uganda da Tanzania wadanda daga baya suka samu horo na mako biyu da ya hada da hawan igiya, yada sansani da dare da kuma lakantar sanin amfani da kayayyakin tsauni. Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS Image copyright PAUL LATHAM/SIGHTSAVERS Jaridun Afirka a wannan lokacin sun ba da rahotanni a kan wannan tattaki kuma duka wadanda suka gudanar da tattakin an karbe su a matsayin jarumai. Takalmansu uku da suka sude a yayin tattakin na nan an kafe su a gidan tarihin Uganda. Copyright © 2019 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba.

No comments:

Post a Comment